Isa ga babban shafi
Najeriya

Dangote ya sake rufe kamfanin sarrafa tumatur a Lagos

Attajirin Afrika Alhaji Aliko Dangote ya sake rufe kamfaninsa na sarrafa tumatur a Lagos kudancin Najeriya bayan ya rufe na Kano a arewacin kasar. Dangote ya rufe kamfanin ne saboda karancin dalar Amurka da za a shigo da kayayyakin aikin sarrafa tumaturin.

Aliko Dangote, Attajirin Afrika
Aliko Dangote, Attajirin Afrika REUTERS/Denis Balibouse
Talla

Wannan kuma koma-baya ne ga gwamnatin Muhammadu Buhari da ke kokarin karkatar da tattalin arzikin Najeriya daga dogaro da arzikin fetir.

A taron tattalin arziki da ake gudanarwa a Davos, Mataimakin shugaban Najeriya Yemi Osinbajo ya ce za su yi kokarin magance wagegen gibin da ake samu a kasuwar canji tsakanin farashin gwamnati da na kasuwar bayan fage.

Tsadar Dala da karancinta ya kuma sa Dangote ya dakatar da wasu kasuwancinsa na kayayyakin abinci da suka shafi Suga da fulawa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.