Isa ga babban shafi
Najeriya

NUPENG ta janye yajin aiki

Kungiyar ma’aikatan mai da kuma gas NUPENG ta dakatar da yajin aikin gargadi na kwanaki uku da ta fara a jiya Laraba, bayan wata ganawa da aka yi tsakanin shugabannin kungiyar da kuma jami’an gwamnati.

Yajin aikin NUPENG zai haifar da matsalar karancin mai a sassan Najeriya
Yajin aikin NUPENG zai haifar da matsalar karancin mai a sassan Najeriya AFP PHOTO/PIUS UTOMI EKPEI
Talla

Kungiyar wadda ta fara yajin aiki domin nuna rashin amincewa da korar wasu mambobinta da kamfanonin mai na Exxon Mobil da Chevron, suka yi, ta yanke shawarar dakatar da yajin aikin ne bayan wata tawaga karkashin jagorancin shugabanta Igwe Achese ta gana da ministan kwadago na Najeriya Chris Ngige a birnin Abuja.

NUPENG ta ce ta janye yajin aikin ne bayan yarjejeniyar da suka amince da kamfanonin karkashin jagorancin Ministan kwadago.

Kungiyar ta ce tana fatar kamfanonin za su mutunta yarjejeniyar inda Minista ya ba su mako biyu su gaggauta biyan bukatun ma’aikatan da suka kora.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.