Isa ga babban shafi
Najeriya

Martanin ‘Yan Shi ‘a ga sakon Buhari na sabuwar shekara

Magoya bayan Ibrahim Zakzaki a Najeriya sun mayarwa shugaba Muhammadu Buhari da martani bayan a cikin sakon shi na sabuwar ya bukaci mabiyan na Shi’a su rungumi zaman lafiya tare da bin dokokin kasa.

Daruruwan 'Yan Shi'a aka kashe a rikicinsu da Sojojin Najeirya a Zaria
Daruruwan 'Yan Shi'a aka kashe a rikicinsu da Sojojin Najeirya a Zaria REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

A sakon da ya aike wa al’ummar kasar dangane da shiga sabuwar shekara ta 2017 shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya bukaci mabiya Shi’a da kuma wadanda ke dauke da makamai a yankin Niger Delta da su rungumi zaman lafiya, sannan kuma su kasance masu mutunta dokokin kasar.

Amma Ibrahim Musa Kakakin ‘yan Shi’ar a Najeriya, ya ce dama su mutane ne masu kaunar zaman lafiya.

"Duk da kisan da aka yi wa mutanenmu amma ba mu dauki doka a hannunmu ba, muna ci gaba da bin hanyoyi na lamama". a cewar Ibrahim Musa Al Mizan.

‘Yan Shi’ar sun ce Shugaba Buhari ne suke bukatar ya kasance mai bin doka da oda bayan Kotu ta bayar da umurnin a saki jagoransu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.