Isa ga babban shafi
Najeriya-Boko Haram

Babu sauran mayakan Boko Haram a dajin Sambisa

Dakarun sojin Najeriya sun yi nasarar fatattakar mayakan Boko Haram daga mabuyarsu da ke dajin Sambisa kamar yadda shugaban kasar Muhammadu Buhari ya fadi a wata sanarwar da aka fitar.

Dakarun sojin Najeriya sun kwashi makonni a farmakin kakkabe Boko Haram daga dajin Sambisa.
Dakarun sojin Najeriya sun kwashi makonni a farmakin kakkabe Boko Haram daga dajin Sambisa. naij.com
Talla

Shugaba Buhari ya ce mayakan ba su da sauran mafaka ganin wannan shine wurin da ya rage musu kafin sojojin su fatattake su.

A jiya juma’a aka yi nasarar kakkabe mayakan daga dajin kamar yadda ya ke kunshe a cikin sanarwar da shugaban ya fitar

Dakarun sojin Najeriya sun kwashi tsawon makonni a farmakin da suka kaddamar kan mabuyar mayakan da ake ganin shine mabuyarsu daya tilo da ya rage a dajin na Sambisa da ke jahar Borno a Arewa maso gabashin kasar.

Shugaba Buhari ya kuma taya sojojin murna game da wannan nasarar da suka samu wajen cin karfin mayakan Boko Haram da suka yi saura.

Mutane akalla dubu goma ne suka rasa rayukansu sanadiyar hare-haren mayakan Boko Haram baya ga wasu fiye da milyan biyu da suka rasa matsuguninsu tun bayan bullar kungiyar a Najeriya
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.