Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Yau shekaru uku da fara yakin Sudan ta Kudu

Yau Sudan ta Kudu ke cika shekaru 3 da fara yakin basasar da ya lakume rayukan dubban mutane tare da tilasta wa kimanin miliyan biyu kaurace wa gidajensu.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir a babban birnin Juba
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir a babban birnin Juba REUTERS/Jok Solomon
Talla

Shugaban kasar Salva Kiir, da ke rikici da jagoran 'yan adawa Riek Machar ya bukaci gudanar da  zaman tattaunawar samar da zaman lafiya mai daurewa a kasar

Kiir, ya ce makasudin bijiro  da wannan bukata, shi ne ceto kasar daga rugejewa baki daya.

Ana dai zargin dakarun Kirr da mayakan da ke goyon bayansa da yin sanadin asarar rayukan jama'a da dama, baya ga  fyade da cin zarafi, da kuma koyawa yara daukan makamai.

Majalisar Dinkin Duniya ta gargadi cewa, kazancewar rikicin kasar na iya kai wa ga kisan kare dangi ko kuma shafe wata kabila.

A bangare guda, kasar Afrika ta Kudu ta yi wa shugaban ‘yan tawayen kasar, Riek Machar daurin talala, a wani mataki na hana shi rura wutar rikicin kasar.

Majiyoyin diflomasiya sun ce, an yi wa Machar daurin ne a kusa da birnin Pretoria, in da ake sanya ido kan zirga-zirgarsa da kuma mu’amalarsa da wayar tarho.

Majioyoyin sun ce, matakin hana Machar zirga-zirga daga wannan kasa zuwa wata kasar, zai rage wa kungiyarsa ta SPLA-IO armashi wadda ta shafe shekaru uku tana fada da bangaren shugaba Salva Kiir.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.