Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu zata fuskanci takunkumin sayan makamai

Kasar Amurka ta gabatar da bukatar sanyawa Sudan ta kudu takunkumin sayen makamai, sakamakon cigaba da samun tabarbarewar tsaro a kasar, wanda tace zai iya kaiwa ga samun kisan kare dangi.

'Yan sandan kwantar da tarzoma cikin shirin ko ta kwana a Sudan ta Kudu
'Yan sandan kwantar da tarzoma cikin shirin ko ta kwana a Sudan ta Kudu UN Photo/Paul Banks
Talla

Jakadiyar Amurka, Samantha Power tace rashin daukar mataki kan Sudan ta Kudu, na iya haifar da fadar kabilancin da ba’a taba gani ba a yankin.

Mai bawa Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya shawara kan hana kisan kare dangi, Adama Dieng yace duk alamun tashin hankali sun tabbata, ganin yadda kasar ta rabe tsakanin kabilun Dinka dake goyawa Salva Kiir bay ada Nuer dake goyan bayan shugaban yan Tawaye Riek Machar.

Kwamitin tsaro na Majalisar Dinkin Duniya ya dade yana barazanar kakabawa Sudan ta Kudu takunkumin sayan makamai, sai dai kasashen Rasha da China da suke da kujerar dindindin a kwamitin na jan kafa wajen zartar da hukuncin, bisa cewa ba lallai bane matakin yayi tasiri.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.