Isa ga babban shafi
Afrika ta Kudu

Ministocin Afrika ta kudu uku sun yanke kauna da Zuma

Wasu ministoci guda uku a Afrika ta kudu sun bukaci shugaban kasar Jacob Zuma ya yi murabus. Wannan na zuwa bayan shafe dare ana muhawara a wani taron shugabannin jam’iyyarsa ta ANC mai mulki akan makomarsa.

Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma
Shugaban kasar Afrika ta Kudu, Jacob Zuma REUTERS/Siphiwe Sibeko
Talla

Ministocin da suka bukaci Zuma ya yi murabus sun hada da na ma’aikatar yawon bude ido da na lafiya da kuma na ayyuka kamar yadda kamfanin dillacin labaran kasar na news24 ya ruwaito daga majiyoyin jam’iyyar ANC mai mulki a kasar.

Wannan na zuwa a muhawarar ta kaure a zauren taron shugabannin jam’iyyar ta ANC akan makomar shugaba Jacob Zuma tun a karshen mako zuwa Litinin.

Zuma dai na fuskantar zarge-zagen rashawa da suka hada da yin amfani da kudaden jama’a wajen yalwata gidansa.

Sau uku kuma shugaban na tsallake kuri’ar yanke kauna a majalisar Afrika ta kudu, wanda ke nuna yana da sauran karfin magoya baya a jam’iyyarsa ta ANC.

Sai dai yana fuskantar adawa daga kungiyoyin kwadago da na farar hula da ‘yan kasuwa da kuma wasu ‘yan jam’iyyarsa ta ANC.

Sai 2019 ne wa’adin shugabancin Jacob Zuma zai kawo karshe, amma a badi ne jam’iyyar shi ta ANC za ta zabi sabon shugaba wanda zai iya kawo karshen mulkin shugaban.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.