Isa ga babban shafi
Najeriya

PDP ta bukaci a dage zaben gwamnan Jihar Ondo

Jam’iyyar PDP da ke adawa a Najeriya ta bukci hukumar Zabe ta dage zaben gwamnan Jihar Ondo da za a gudanar a ranar 26 ga wannan watan nan Nuwamba har sai kotu ta tabbatar da dan takarar jam’iyyar tsakanin Eyitayo Jegede da Jimoh Ibrahim.

Tutar jama'iyar PDP mai adawa a Najeriya
Tutar jama'iyar PDP mai adawa a Najeriya
Talla

PDP ta nemi dage zaben ne saboda rikicin Jam’iyyar inda mutane biyu ke ikirarin zama ‘Yan takara gwamnan Jihar ta Ondo.

Wannan kuma na zuwa ne bayan kotun daukaka kara a Abuja ta dage zartar da hukunci akan koken da Eyitayo Jegede ya shigar na tabbatar da shi a matsayin dan takarar gwamna sabaniin Jimoh Ibrahim da kotun Tarayya ta tabbatar a matsayin dan takarar gwammnan na PDP.

Jimoh Ibrahim dai na bangaren shugabancin Senata Ali Modu sheriff, yayin da Jegede ke bangaren Senata Ahmed Makarfi da ke hamayya da Sherif a shugabancin Jam’iyyar na kasa.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.