Isa ga babban shafi
Najeriya

Kotun daukaka kara taki yanke hukunci kan shari'ar PDP

Kotun daukaka karar Najeriya taki yanke hukunci kan rikicin shugabancin Jam’iyyar PDP wanda bangaren Sanata Ahmed Makarfi ya shigar.

Sanata Ahmed Makarfi shugaban rikon kwarya na jam'iyyar PDP.
Sanata Ahmed Makarfi shugaban rikon kwarya na jam'iyyar PDP. bellanaija
Talla

Makarfi ya ruga kotun daukaka karar ne dan tabbatar da hukunci wata kotu ta dabam da ta amince da shugabancinsa, yayin da wata kotu makamanciyar wancan tace Sanata Ali Modu Sharif ne shugaba.

Shugabar alkalan kotun, Jummai Sankey tace sun dauki matakin ne saboda zargin nuna san kai da aka musu.

Wannan ba karamar koma baya bane ga Jam’iyyar PDP wanda ke shirin zuwa zaben Gwamnan Jihar Ondo a wannan watan.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.