Isa ga babban shafi
Najeriya

Tsohon Sarkin Musulmi Ibrahim Dasuki ya rasu

Allah Ya yi wa Tsohon Sarkin Musulmin Najeriya, Ibrahim Dasuki rasuwa yana da shekaru 93 sakamakon rashin lafiya. Za a yi Jana’izar shi a yau Talata. Dasuki shi ne Sarkin Musulmi na 18, wada ya yi shekaru 8 akan karagar mulki kafin tsohon shugaban kasa marigayi Janar Sani Abacha ya tube shi.

Marigayi tsohon Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Ibrahim Dasuki
Marigayi tsohon Sarkin Musulmin Najeriya Alhaji Ibrahim Dasuki premiumtimes
Talla

Tsohon Shugaban kasa Janar Ibrahim Badamasi Babangida ne ya nada Alhaji Ibrahim Dasuki a matsayin Sarkin Musulmi na 18 bayan rasuwar Abubakar na uku.

Dasuki ya yi sarauta tsakanin 6 ga watan Disamba na shekarar 1988 zuwa 20 ga watan Afrilu na shekarar 1996.

Marigayi Dasuki gogaggen ma’aikacin gwamnati ne da ya yi aiki tare da Sardaunan Sakkwato Ahmadu Bello.

Tsohon Sarkin shi ne mahaifin Kanal Sambo Dasuki, tsohon mai bai wa shugaban kasa Goodluck Jonathan shawara kan harkokin tsaro.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.