Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

Cote d’Ivoire ta fara aiki da sabon kundin tsarin mulki

Cote d’Ivoire ta fara aiki da sabon kundin tsarin mulki da ya samu amincewar ‘yan kasar a zaben raba gardama bayan Shugaba Alassane Ouattara ya sanya hannu kan sabon kundin tsarin mulkin a ranar Litinin.

Zaben raba gardama akan sabon kundin tsarin mulki a Cote d'Ivoire
Zaben raba gardama akan sabon kundin tsarin mulki a Cote d'Ivoire REUTERS/Luc Gnago
Talla

Yayin da ya ke jawabi wajen bikin, Ouattara ya ce yanzu haka guguwar siyasa ta fara kadawa a cikin kasar, tare da bayyana fatar samun dorewar zaman lafiya da cikkaken ‘yanci da a mutunta juna.

A cikin sabon kundin an cire ayar dokar da ke magana kan sai iyayen mutum sun kasance ‘yan asalin Cote d’Ivoire kafin ya tsaya takarar shugaban kasa.

Kashi 93 na masu zabe ne suka amince da sabon kundin wanda yan adawa suka kauracewa kada kuri’a.

‘Yan adawar suna sukar sabon kundin ne da suke ganin Ouattara na son ya dora wanda zai gaje shi ne.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.