Isa ga babban shafi
Cote d'Ivoire

An amince da sabon kundin tsarin mulki a Cote d’Ivoire

Hukumar zabe a kasar Cote d’Ivoire ta ce sama da kashi 93 na masu jefa kuri’a a kasar suka amince da sabon kundin tsarin mulki a zaben raba gardamar da aka gudanar a karshen mako.

'Yan adawa sun kauracewa zaben raba gardama domin sauya kundin tsarin mulki
'Yan adawa sun kauracewa zaben raba gardama domin sauya kundin tsarin mulki REUTERS/Luc Gnago
Talla

Sakamakon hukumar zaben ya ce, kashi 42 na ‘Yan kasa suka shiga zaben, kuma sama da kashi 93 suka goyi bayan sabon kundin tsarin mulkin.

Amma ‘Yan adawar kasar sun kauracewa zaben tare da zargin an yi magudi a kuri’ar da aka jefa ta raba gardama.

Sabon kundin tsarin mulkin ya kunshi kirkiro da mataimakin shugaban kasa da Majalisar Dattijai inda ‘Yan adawa ke zargin shugaba Ouattara na son dora wanda zai gaje shi ne.

Tuni dai Majalisar wakilan kasar ta amince da sabon kundin tsarin mulkin wanda gwamnatin Alassane Ouattara ke cewa kirkiro da mataimakin shugaban kasa zai bayar da damar ci gaba da tafiyar da mulki idan shugaban kasa ya gaza ko ya mutu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.