Isa ga babban shafi
Sudan ta Kudu

Sudan ta Kudu ta rufe babban gidan Jarida a kasar

Gwamnatin Sudan ta Kudu ta Rufe wani babban gidan Jarida da ke kasar, wanda ya wallafa labari game da wani rahoto da ke nuna cewa jami’an gwamnatin kasar suna amfani da rikicin kasar wajen azurta kansu.

Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir
Shugaban Sudan ta Kudu Salva Kiir Charles Atiki Lomodong / AFP
Talla

Babban eidtan jaridar mai suna National Mirror Simon Aurelious ya ce jami’ai daga hukumar binciken bayanan sirri ta kasar suka garkame gidan jaridar basu sanar da su makasudin daukar matakin ba.

Aurelious ya ce an dai gayyace su zuwa shedikwatar hukumar inda aka nuna musu takardar izinin rufe gidan jaridar daga gwamnati.

A ranakun talata da laraba dai Jaridar ta National Mirror ta wallafa rohoton da wani shararren dan fim na kasar Amurka Goerge Clooney ya fitar, wanda ya zargi gwamnatin Sudan ta Kudu da bangaren ‘yan tawaye karkashin riek machar da satar dukiyar kasa ta hanyar fakewa da rikincin da ya barke tsakaninsu.

Matakin rufe jaridar ya zo kwanaki kadan bayan da Majalisar Dinkin Duniya ta bayyana damuwa, bisa yadda ta ce gwamnatin Sudan ta Kudu tana barazana ga kungiyoyin fararen hula masu rajin kare hakkin dan’adam.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.