Isa ga babban shafi
South Sudan- Sudan

Sabon Mataimakin Shugaban Sudan ta Kudu na ziyarar a Khartoum

Sabon mataimakin shugaban kasar Sudan ta Kudu Taban Deng Gain na shirin tafiya kasar Sudan gobe lahadi domin ziyara ta kwanaki biyu inda ake sa ran ya tattauna batutuwa da dama da jami'an Khartoum.

Sabon Mataimakin Shugaban Sudan ta Kudu Taban Dang Gai.
Sabon Mataimakin Shugaban Sudan ta Kudu Taban Dang Gai. REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Ziyarar tasa ita ce ta farko tun bayan hawansa kujeran mataimakin shugaban Sudan ta Kudu.

Jakadan Sudan ta kudu a Khartoum,  Mayan Dout ya shaidawa kamfanin Dillancin labaran Faransa AFP cewa wasu ministoci da mashawartan Shugaba Salva Kiir zasu rufa masa baya a tattaunawan irin sa na farko don warware wasu batutuwa da ba'a warware ba  tun bayan samun 'yanci..

Gwamnatin Salva Kiir har yanzu bata ce ga inda tsohon mataimakin shugaban kasar Reik Machal yake ba.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.