Isa ga babban shafi
Zambia

An kame masu zanga zanga 133

‘Yan sanda a kasar Zambia su kame mutane 133 da ke gudanar da zanga zangar nuna adawa da sake nasarar zabar shugaban kasa mai ci Edgar Lungu. 

Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu
Shugaban kasar Zambia Edgar Lungu
Talla

Baturen ‘yan sandan lardin kudancin kasar Godwin Phiri ya ce sun kame masu zanga zangar ne saboda hare haren da suke kaiwa kan magoya bayan jam’iyya mai mulki ta (PF) tare da lalata musu dukiya.

Phiri ya ce tarzomar ta lafa bayan kamen da jami’an tsaro suka yi.

Edgar Lungu karkashin Jam’iyyar (PF) ya samu nasara da kashi 50.35% na kuri’un da aka kada, yayinda jagoran ‘yan adawa Hichilema ya samu kashi 47.67% karkashin Jam’iyyar adawa ta (UPND), kamar yadda hukumar zaben Zambia ta sanar.

Edgar Lungu zai sake shafe shekaru biyar yana shugabantar kasar Zambia kafin wa'adinsa ya kare.

 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.