Isa ga babban shafi
Afika ta kudu

ANC ta sha kayi a Pretoria na Afrika ta Kudu

Jam’iyyar ANC mai mulkin Afrika ta Kudu ta sha kayin da ba ta taba ganin irinsa ba a tarihin siyasar kasar, bayan jam’iyyar adawa ta Democratic Alliance ta doke ta a birnin Pretoria a zaben kananan hukumomi da aka gudanar.

A karon farko cikin shekaru 22 jam'iyyar ANC ta Afrika ta Kudu ta sha kayin da ba ta taba ganin irinsa ba a tarihin siyasar kasar
A karon farko cikin shekaru 22 jam'iyyar ANC ta Afrika ta Kudu ta sha kayin da ba ta taba ganin irinsa ba a tarihin siyasar kasar RAJESH JANTILAL / AFP
Talla

Hukumar zaben kasar ta ce, jam’iyyar adawar ta samu kashi 43.1 cikin 100 yayin da ANC ta samu kashi 41.2 cikin 100 a yankin Tshwane wanda ke kunshe da birnin Pretoria.

Wannan dai na kara nuna yadda al’ummar kasar suka dawo daga rakiyar jam’iyyar ta ANC wadda ta shafe tsawon shekaru 22 akan karagar mulki tun bayan kawo karshen mulkin wariyar launin fata a shekara ta 1994.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.