Uganda
Uganda ta samu mutane 7 da laifi wajen kai wa kasar harin ta'addanci
Kotun kasar Uganda ta samu mutane 7 da laifi wajen kai wa kasar harin ta’addanci wanda ya yi sanadiyyar mutuwar mutane 76 a shekara ta 2010.
Wallafawa ranar:
Talla
A jimilce dai mutane 13 ne ake zargi da hannu wajen tarwatsa bama-bamai akan wani taron jama’a da ke kallon kwallo a birnin Kampala, harin da kungiyar Al-shabab ta ce magoya bayanta ne suka kais hi.
Tuni dai kotun ta wanke sauran mutane 6 saboda rashin cikakkiyar shaida a kansu.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu