Isa ga babban shafi
Mali

An kai sabon harin bindiga a birnin Bamako na kasar Mali

An sake kai wani sabon harin a birnin Bamako dake kasar Mali, kamar yadda rahotanni ke cewa yanzu haka wasu da ba’a san ko su waye ba sun bude wuta akan sansanin sojin kungiyar kasashen Turai dake birnin na Bamako.

Bamako,babban birnin kasar Mali.
Bamako,babban birnin kasar Mali. HABIBOU KOUYATE / AFP
Talla

Wakilin kamfanin dillancin labaran Faransa da wasu mutane a Bamako sun tabbatar da ganin harin wanda yanzu haka yake gudana inda ake jin karan harbe harbe.

kasar Mali da sauran kasashen dake makwabtaka da ita na ci gaba da fuskantar hare-haren ta'addanci sakamakon ayyukan kungiyoyi masu tayar da kayar baya a yankunan al'amarin da ya kai ga rasa rayukan mutane da dama yawanci kuwa baki ne yan kasashen waje da suke yawon bude ido a nahiyar Afrika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.