Isa ga babban shafi
Faransa

Ayrault da Cazeneuve sun isa Cote d’Ivoire

Ministocin ciki da na wajen Faransa sun isa kasar Cote d’Ivoire domin nuna goyon baya tare da jajanta mumunar harin da ya hallaka mutane 18 cikin har da Faransawa 4.

Ministan harakokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault da takwaransa na cikin gida Bernard Cazeneuve a Cote d'Ivoire
Ministan harakokin wajen Faransa Jean-Marc Ayrault da takwaransa na cikin gida Bernard Cazeneuve a Cote d'Ivoire ISSOUF SANOGO / AFP
Talla

Tuni kungiyar al Qaeda ta dau alhakin harin da aka kai a gabar ruwan Granda Bassam da ke Cote d’voire.

Kuma Ziyarar Ministocin biyu Jean Marc Ayrault da Bernard Cazeneuve a Cote d’voire na zuwa ne a dai-dai lokaci da kungiyar al-qaeda ta mika sakon barazanar ga Faransa da kasashen yankin Sahel aminnan kasar.

A cewar Mayakan na Al-qeda harin Grand Bassam gargadi ne ga Faransa da ke jagoranta rundunar yaki da ta’addanci a yankunan Sahel da suka hada da Burkina Faso da Chadi da Mali da Mauritania da Nijar.

Al-qeda ta kuma gargadi Cote d’Ivoire da duk ‘yan kasashen Faransada wasu na kasashen yammacin da ke zaune a kasar, inda tace zata ci gaba da zama barazana ga tsaron Cote d’Ivoire.

A Janairu Kungiyar ta dau alhakin mumunan hare haren Otel Burkina Faso wanda ya kashe mutane 30, da kuma harin Bamako inda mutane 20 suka mutu.

Faransa dai ta tabbatar da goyon bayanta ga cote d voire da sauran kasashen Sahel wajen yaki da ta’addanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.