Shugabannin kasashen Africa na taro a Masar game da bunkasa tattalin arziki
Shugaban kasar Masar Abdel Fattah al-sisi yau asabar ya bude wani babban taron bunkasa tattalin arzikin kasashen Africa, dake samun halarcin shugabannin kasashen Africa da wasu fitattun ‘yan kasuwa na nahiyar.
Wallafawa ranar:
Taron wanda aka saba yi na kwanaki biyu a wajen shakatawa na Sharm-el Sheikh na samun halarcin wakilai dubu da dari biyu.
Masana kan rika cewa duk da bunkasar da nahiyar Africa ta yi, harkokin ciiniki da kasuwancin nahiyar bai wuce kashi biyu daga cikin dari ba na harkokin ciniki da kasuwanci na duniya.
Shugabannin kasashen da suka halarci taron sun nemi masu zuba jari da su zuba jarin su wajen habaka nahiyar ba tare da fargaban halin ta'addanci da wasu kasashen nahiyar ke fama dashi ba.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu