Isa ga babban shafi
Chad

Shugaba Deby ya nada sabon Firaminista

Shugaban kasar Chadi Idriss Deby ya nada sabon Firaminista a daren jiya asabar,Pahimi Padacke Albert ne mutumen da shugaban ya zaba da kuma zai shugabantar gwamantin kasar. 

Shugaban Chadi Idriss Deby
Shugaban Chadi Idriss Deby REUTERS/Tiksa Negeri
Talla

Raba gari da Shugaban kasar yayi da tsohon firaminista Kalezeube Pahimi Debeu wata alama ce dake tabbatar da cewa duk ya ‘an jam’iyyar MPS mai mulkin kasar da suka nuna adawa da shirin shugaba Deby na sake tsayawa takara a zaben shugabancin kasar na ranar 10 ga watan Afrilu mai zuwa rabuwa da su ya fi zama alheri a cewar majiyoyi da dama a fadar Shugaban kasar dake Djamena.
Shugaban kasar Chadi Idris Deby ya karbi raggamar shugabanci kasar ne a wani juyin mulki da yayiwa Hissen Habre a shekara ta 1990.
Wa’adi na biyar kenan da Deby zai shugabantar kasar har in ya lashe zaben dake tafe.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.