Isa ga babban shafi
Burkina Faso

Kabore ya kafa Majalisar ministoci mai mambobi 29

Sabon Firaiyi ministan Burkina Faso Paul Kaba Thieba, ya kafa majalisar ministoci mai mambobi 29 cikinsu har da mata 7, sai dai shugaban kasar Roch Marc Christinane Kabore ne zai rike mukamin ministan tsaron kasar.

Firaiyi ministan Burkina Faso Paul Kaba Thieba.
Firaiyi ministan Burkina Faso Paul Kaba Thieba. AFP/AHMED OUOBA
Talla

A karkashin wannan sabuwar majalisar ministocin, an nada tsohon magajin garin birnin Ouagadougou Simon Compaore a matsayin sabon ministan cikin gida, yayin da aka nada Alpha Barry tsohon wakilin rfi a matsayin ministan harkokin waje.

Zababben shugaban kasar Roch Marc Christian Kabore dai ya yi alkawarin sake gina Burkina Faso ta hanyar kawo karshen zaman kashe wando da matasan kasar da dama ke yi tare da inganta sashen ilimi da asibitoci a kasar da kashi 46 daga cikin 100 ke fama da talauci.
 

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.