Isa ga babban shafi
Masar

An bude majalisar Masar

A Karon farko a cikin shekaru uku an bude Majalisar kasar Masar mai dauke da yan Majalisu 596 da ake sa ran za ta taka rawa wajen tabbatar da dimokiradiya a kasar mai fama da rikicin siyasa.

An bude Majalisar Masar a karon farko tun  kawar da gwamnatin Morsi shekaru uku da suka gabata
An bude Majalisar Masar a karon farko tun kawar da gwamnatin Morsi shekaru uku da suka gabata REUTERS
Talla

Majalisar ta zabi Farfesa Ali Abdel-Al a matsayin shugabanta, kuma ana sa ran ta fara aiki gadan-gadan wajen duba sabbin dokokin kasar.

An dai rusa Majalisar ce a shekarar 2012 bayan kawar da zababben shugaba na farko Mohammed Morsi na ‘Yan uwa musulmi.

A ranar Lahadi ne aka rantsar da ‘Yan majalisun, amma wasunsu da dama tutar Masar suka rike a yayin rantsuwar.

Bude Majalisar na zuwa ne a yayin da kasar ke fama da matsalar tsaro da barazanar hare haren ‘Yan ta’adda.

Gwamnatin Masar tace zata karfafa matakan tsaro a kasar domin kare lafiyar baki ‘yan yawaon bude ido bayan wani harin da ya raunana ‘Yan kasashe waje 3 ranar juma’a.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.