Isa ga babban shafi
Mauritania

Dan al Qaeda ya tsere daga gidan yarin Mauritania

Wani dan kasar Mauritania da aka yankewa hukuncin kisa sakamakon samunsa da laifin ta’addanci ya tsere daga gidan yarin da ake tsare da shi a birnin Nouakchott na Mauritania.

Shugaban Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz
Shugaban Mauritania Mohamed Ould Abdel Aziz AFP PHOTO / WATT ABELJELIL
Talla

Sheick Ould Saleck an yanke masa hukuncin kisa ne tun a shekara ta 2011, bayan da aka same shi da laifin yunkurin hallaka shugaban kasar Mohammed Ould Abdul’aziz bisa umurnin kungiyar Al Qaeda.

Rahotanni sun ce Sheick ya tsere ne daga gidan yarin Nouakchott tun a ranar Alhamis, sai dai ba a fahimci cewa ba ya cikin gidan kurkukun ba sai da lokacin sallar Azahar ya yi ba tare da ya zo masallaci ba.

Daga bisani dai jami’an gidan yarin sun tarar cewa ba ya cikin dakin da ake tsare da shi, yayin da wasu bayanan ke cewa an tarar da tutar Kuungiyar Aqmi reshen Al Qaeda a magreb da sahel a cikin dakin.

Lokacin da magoya bayan kungiyar Al Qaeda suka yi yunkurin hallaka shugaba AbdulAziz a 2011, an yi musayar wuta a wata unguwa da ke wajen birnin Nouakchott har aka kashe jami’in tsaro daya da kuma ‘yan bindiga 4.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.