Isa ga babban shafi
Bakonmu a Yau

Sake gina arewacin Najeriya

Wallafawa ranar:

A makon da ya gabata ne shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya sanar da kafa kwamitin dai zai gudanar da aikin sake gina yankin Arewa Maso gabashin kasar wanda ayyukan Boko Haram suka yi sanadiyyar yanzu haka sama da mutane milyan biyu suka kauracewa.Wasu daga cikin ayyukan kwamitin wanda zai kasance karkashin jagorancin Attajiri Janar Theopilius Yukubu Danjuma mai ritaya sun hada da tattara kudaden taimaka a cikin da wajen kasar, da kuma shata yadda za a ake gina irin barnar da Boko Haram ta haddasa wa yankin.Hon Muhammad Sani Zoro, shi ne shugaban Kwamitin kula da wadanda rikicin na Boko Haram ya shafa a Majalisar wakilan kasar, ya ce duk da yake an dauki dogon lokaci kafin a kafa shi, to amma wannan kwamitin zai taimaka wajen raye yankin da lamarin ya shafa. 

Tutar Tarrayar Najeriya
Tutar Tarrayar Najeriya
Sauran kashi-kashi
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.