YanTawayen Afrika ta Tsakiya sun kafa yanki mai cin gashin kan sa
Shugaban ‘yan tawayen Seleka na jamhuriyar Afrika ta tsakiya, Noureddine Adam ya sanar da kafa yanki mai cin gashin kan sa a arewa maso gabashin kasar, a dai dai lokacin da ake shirin gudanar da zabe a ranar 27 ga watan disemba.
Wallafawa ranar:
Mai Magana da yahu shugaban ‘yan tawayen Seleka, Maouloud Moussa ya ce, a jiya litinin ne suka ayyana yankin Logone da ke garin Kaga-Bandoro a matsayin jamhuriya mai cin gashin kai.
Shugaban ‘yan tawayen Seleka dai ya yi watsi da shirin zaben kasar wanda ake fatan zai kawo zaman lafiya a Jamhuriyar Afrika ta Tsakiya.
Jamhuriyar Afrka ta Tsakiya na daga cikin kasashen Afrika da talauci ya yiwa kanta.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu