Isa ga babban shafi
Rwanda

Rwanda za ta yi zaben raba gardama

Kasar Rwanda za ta gudanar da zaben raba gardama nan da mako mai zuwa game da sauye sauyen kundin tsarin mulkin kasar domin bai wa shugaba Paul Kagame damar ci gaba da zama akan karagar mulki har zuwa shekara ta 2034.

Shugaba Paul Kagame na Rwanda.
Shugaba Paul Kagame na Rwanda. REUTERS/Ruben Sprich
Talla

Gwamnatin kasar ta bayyana cewa an yake shawarar gudanar da zaben ne a taron majalisar ministocin kasar da aka gudanar a jiya talata, kuma an tsayar da ranar 18 ga watan Disamba domin yin zaben yayin da kuma ‘yan asalin kasar da ke zaune a kasashen ketere za su yi nasu zaben a ranar 17 ga watan.

Mista Kagame ne ya jagoranci zaman majalisar ministocin kuma shi ne shugaban Afrika na baya-bayan nan da ke kokarin tsawaita zamansa a kan karagar mulki.

Irin wannan yunkurin dai ya haifar da tarzoma a kasashen Burundi da Burkina Faso da Jamhuriyar Demokradiyyar Congo, amma dai kawo yanzu babu alamar rikici a kasar Rwanda.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.