Isa ga babban shafi
Libya

Bangarorin Libya sun amince su sasanta

Bangarorin da ke rikici a Libya sun ce sun cim ma yarjejeniya a tattaunawar sulhu da suke gudanarwa a Tunisia domin kawo karshen tashin hankalin da kasar ta shiga tun kawar da gwamnatin Kanal Gaddafi.

Tun kawar da gwamnatin Ghaddafi Libya ta fada cikin rikici
Tun kawar da gwamnatin Ghaddafi Libya ta fada cikin rikici AFP
Talla

Tattaunawar ta kunshi bangaren gwamnatin da ke iko a Tripoli da kuma bangaren da ke shugabanci a gabashin kasar.

Bangarorin biyu sun amince a zabo wakilai tsakaninsu da zasu kafa kwamiti domin zaben sabon Firaminista nan da kwanaki 15, sannan za a samar da wani kwamiti da zai diba kundin tsarin mulki.

Sai dai kuma duk da wannan matakin, wasu na ganin sai bangarorin biyu sun yi maganin mayakan IS da suka samu wurin zama birnin Sirte.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.