An kai harin kunar bakin wake a Kamaru
Hukumomin tsaro na kasar Kamaru sun bayyana cewa wasu mutane da ake zaton mayakan Boko Haram ne sun kaddamar da hare haren kunar bakin wake a yankin arewacin kasar, inda akalla mutane uku suka rasa rayukansu.
Wallafawa ranar:
An kaddamar da jerin hare haren ne guda biyu a cikin daren jiya a Waza da ke yankin arewa mai nisa yayin da wasu rahotannin ke cewa adadin wadanda suka rasu ya kai shida.
A bangare guda, jami’an tsaro sun yi nasarar hallaka wata ‘yar kunar bakin waken dabam da ta yi yunkurin tayar da bam din da ke jikinta.
Kungiyar Boko Haram dai ta sha tura ‘yan mata domin kaddamar da harin kunar bakin wake a Kamaru kuma al-amarin na neman zama ruwan dare.
Kasar Kamaru na cikin kasashen yankin tafkin Chadi da ke kokarin kawo karshen kungiyar Boko Haram wadda ta hallaka mutane da dama.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu