Shugaba Alpha Conde ya salami Ministan cikin gida
Shugaba Alpha Conde na kasar Guinea Conakry ya tube ministan cikin gidan kasar da kuma wasu manyan jami’an gwmanatinsa biyu daga mukamansu saboda sakaci har aka samu asarar rayyukan jama’a a wani rikici dangane da gina masallaci a garin Touba.
Wallafawa ranar:
Ministan cikin gida Mahmoud Cisse, sakataren kasa mai kula da sha’anin addinai,Alhaji Abdoulaye Diassy da mataimakinsa Aboubacar Fofana, shugaban kasar ya tube su ne bayan da aka samu asarar rayyukan mutane biyu, sakamakon artabun da aka yi tsakanin mazauna gari a lokacin da wasu suka bukaci gina wani sabon masallaci a garin.
Mutane da dama ne suka samu raunuka, yayin da aka kona gidaje da kadarori a lokacin wannan rikici. Tuni dai aka cafke mutane 13 da ake zargi da hannu wajen tayar da rikicin.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu