Isa ga babban shafi
Najeriya

Dakarun Najeriya na ci gaba da samun nasara kan Boko Haram

Sojojin Najeriya dake yakin kawo karshen ayyukan mayakan kungiyar Boko Haram a Maiduguri jihar Borno sun ce sun gano wani wuri da mayyakan suka boye man fetur mai yawan gaske dama wasu kayyaki na su da suka hada da motoci da Babura.

Dakarun Cadi dake fafatakar yan kungiyar Boko Haram
Dakarun Cadi dake fafatakar yan kungiyar Boko Haram AFP PHOTO / PHILIPPE DESMAZES
Talla

kakakin rundunar sojin kasar Kanar Sani Usman kukasheka ne ya sanar da hakan inda yace sun kuma yi nasarar kama wani dan kungiyar mai suna Musa Abba bayan sun sami bayyanai daga wasu mazauna yankin .

Kanar Sani Usman kukasheka yayi kira zuwa mazauna garuruwan Kangallam,Marte dama Abadam da cewa su yi hatara wajen yi amfani da ruwan koguna dana rijiyoyi dake yankunan ,ana zargin yan kungiyar Boko Haram da saka guba a cikin su.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.