Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mugabe ya karanta tsohon jawabi a Majalisar Zimbabwe

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe mai shekaru 91 ya karanta wani tsohon jawabi a zauren Majalisar kasar a jiya Talata, kuskuren da ‘Yan adawa ke ganin ya dace a diba lafiyar shugaban.

Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe
Shugaban Zimbabwe Robert Mugabe REUTERS/Philimon Bulawayo
Talla

Mugabe ya gabatar da tsohon jawabin ne a yayin bude zauren majalisa.

Rahotanni sun ce shugaban ya karanta wani tsohon jawabin da ya taba gabatarwa a ranar 25 ga watan Agusta inda ya ke bayyana fatarsa akan China wajen farfado da tattalin arzikin Zimbabwe.

Shugaban ya gabatar da jawabin ne ba gargada, inda kakakinsa ya daura alhakin kuskuren akan Jami’ansa.

Anan gaba shugaban zai sake karanta sabon jawabin wanda ya dace ya gabatar a zauren Majalisa.

Tuni dai babbar jam’iyyar adawa tace wannan alamu ne da ke nuna gazawar shugaban wanda ke jagorantar Zimbabwe tun 1980, da kasar ta samu ‘yanci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.