Isa ga babban shafi
Zimbabwe

Mugabe ya tube mataimakiyarsa

Shugaban kasar Zimbabwe Robert Mugabe ya tube Mataimakiyarsa Joice Mujuru tare da wasu Ministocinsa guda takwas da ake zargi suna kule kullen hambarar da gwamnatin shugaban mai yawan shekaru a Nahiyar Afrika. Mujuru ta fuskanci kalubale da suka daga Grace Matar shugaba Mugabe.

Mugabe na Zimbabwe tare da Mataimakiyarsa Joice Mujuru
Mugabe na Zimbabwe tare da Mataimakiyarsa Joice Mujuru AFP/Jekesai Njikizana
Talla

Tuni Jam’iyyar ZANU PF ta tube Mujuru daga kwamitin amintattu, akan  zargin tana jagorantar kokarin kashe Mugabe don kwace mulkin kasar Zimbabwe.

Bayan dakatar da Mujuru, Jam’iyyar ZANU PF ta tabbatar da Mugabe a matsayin shugaba tare da zabar matarsa Grace a matsayin shugabar Mata.

Tun samun ‘Yancin kasar Zimbabwe a 1980, Mugabe ke shugabantar kasar.

Mujuru tace zata shigar da kara domin kalubalantar yarfen siyasa da zargin kokarin kisan Mugabe.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.