Bankin raya Afrika zai mayar da hankali ga samar da Lantarki
Sabon shugaban Bankin raya Afrika AFDB, ya ce a shekaru masu zuwa nan gaba, Bankin zai mayar da hankali ne wajen magance matsalar karancin wutar lantarki domin bunkasa tattalin arzikin kasashen Afrika.
Wallafawa ranar:
Matsalar lantarki dai na durkusan da masana’antu a Afrika, al’amarin da ke gurgunta tattalin arzikin kasar, a cewar Akinwumi Adesina.
Ya kara da cewa matsalar na haifar da rashin ayyukan yi ga matasa.
Wasu alkalumma na hukumar makamashi ta duniya sun bayyana cewa Afrika na bukatar kudi da suka kai dala biliyan 450 domin bunkasa lantarki a birane daga nan zuwa shekarar 2040.
Sabon shugaban ya ce magance matsalar makamashi shi ne babban abin da zai sa gaba, kamar yadda ya shaidawa kamfanin dillacin labarain Reuters, a Abidjan.
LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.
Hulda da mu