Isa ga babban shafi
Afrika ta tsakiya

An takaita wa’adin shugabanci zuwa biyu a Afrika ta tsakiya

Gwamnatin Rikon kwaryar Janhuriyar Afirka ta Tsakiya ta amince da sabon kundin tsarin mulki wanda ya kunshi yin wa’adi biyu kawai ga duk wani shugaban kasa.

Shugaban rikon kwarya a Afrika ta tsakiya Alexandre-Ferdinand Nguendet
Shugaban rikon kwarya a Afrika ta tsakiya Alexandre-Ferdinand Nguendet AFP PHOTO ERIC FEFERBERG
Talla

Sabon kundin ya ce shugaban kasa zai yi wa’adin shekaru 5 sau biyu ba tare da kari ba, kuma kundin ya amince a kafa majalisar dattawa.

Shugaban rikon kwaryar Alexandre-Ferdinand Nguendet ya bukaci al’ummar kasar su bai wa kundin goyan bayan da ya dace don magance rikicin kasar.

Kotun kundin tsarin mulki a Afrika ta tsakiya  ta haramtawa duk wani mamba na gwamnatin rikon kwarya tsayawa takara a zaben shugaban kasa ko na ‘Yan majalisu da za a gudanar a watan Oktoba.

Afrika ta tsakiya dia ta fada cikin rikici ne a watan Maris din 2013 tsakanin Mayakan Seleka yawancinsu Musulmi da kuma anti-balaka Kiristoci.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.