Isa ga babban shafi
Mali

Reshen Alqaida ya dauki alhakin kai hari a Mali

Gwamnatin Mali ta kafa kwamitin bincike na kwararru domin gano babbar manufar wadanda suka kai hari a wani otel da ke garin Sevare inda aka share tsawon sa’o’i 24 kafin murkushe ‘yan bindigar.

Ginin otel Byblos da aka kai wa hari a garin Sévaré ranar 8 ga watan agustan 2015 a Mali
Ginin otel Byblos da aka kai wa hari a garin Sévaré ranar 8 ga watan agustan 2015 a Mali AFP PHOTO / STRINGER
Talla

Sanarwar da hukumomin kasar suka fitar ta bayyana cewa mutane 13 suka mutu a lamarin, yayin da aka samu nasarar ceto mutane 4.

Binciken farko dai na nuni da cewa magoya bayan wani malami mai suna Amadou Koufa dan asalin garin Mopti ne suka kai harin, kuma tun da jimawa ne ake zargin malamin da yin alaka da kungiyar Ansr Dine mai nasaba da Alqaida.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.