Isa ga babban shafi
Libya

Mutane 40 sun mutu a rikicin kabilanci a Libya

Akalla mutane 40 aka kashe cikin mako guda a rikici tsakanin kabilun Toubou da Azbinawa masu dauke da makamai a Sabha da ke kudancin kasar Libya yankin Sahara.

Tun kawar da gwamnatin Kanal Ghaddafi kasar Libya ke fama da rikici.
Tun kawar da gwamnatin Kanal Ghaddafi kasar Libya ke fama da rikici. REUTERS/Stringer
Talla

Mahukunatan yankin sun ce rikicin ya tursasawa daruruwan mutane barin gidajensu tun soma rikicin tsakanin kabilun guda biyu a watan Fabrairu.

‘Yan Kabilar Toubou dai na kan iyaka ne da kasar Chadi, wadanda suka dade suna fuskantar wariya tun zamanin mulkin Marigayi Kanal Ghaddafi.

Kuma suna cikin mutanen da suka shiga yakin da aka kawar da tsohon shugaban na Libya a 2011.

Abzinawa kuma na kan iyaka ne da Algeria da kuma Nijar a kudancin Libya wadanda ke goyon bayan marigayi Kanal Ghaddafi.

Kabilun biyu na rikici ne kan arzikin kasa a yankin sahara na Libya, inda bangarorin biyu ke ikirarin iko da yankin.

Libya dai na fama da rikicin Mayaka da dama, kuma yanzu rikicin kasar ya kazance musamman tsakanin mayakan da ke ikirarin tafiyar da gwamnatin kasar a Tripoli da Tabrouk.

Kuma mayakn Abzinawa a yankin Sahara na samun goyon baya daga bangaren gwamnatin Tripoli, yayin da ‘Yan kabilar Toubou ke samun goyon bayan gwamnatin da kasashen duniya ke marawa baya a gabacin kasar.

 

Tun kawar da gwamnatin Kanal Ghaddafi dai kasar Libya ke fama da rikici.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.