Isa ga babban shafi
Mali

An hallaka Mayakan Jihadi a Mali

Dakarun sojan kasar Mali sun hallaka mayakan jihadi da dama a yankin kudancin kasar dake gab da kan iyakarta da kasar Cote d’Ivoire.

Dakarun soin Mali
Dakarun soin Mali AFP/PHILIPPE DESMAZES
Talla

Rahotannin sun ce sojojin sun yi nasara lalata sansanonin mayakan a dajin da ya hada kan iyakokin kasashen biyu, kamar yadda wani hafsan sojan kasar ta Mali ya sanar da kamfanin dillancin labaran Faransa AFP.

Jami’in sojan da ya nemi a sakaya sunansa ya bayyana cewa sun yi fata-fata da mayakan jihadin a sansaninsu da ke cikin dajin Sama a kan iyakokin kasashen biyu inda tare da kama wasu da dama.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.