Isa ga babban shafi
Sudan ta kudu

Kwalara ta hallaka mutane a Sudan ta Kudu

Akalla mutane 18 ne suka rasa rayukansu sakamakon barkewar cutar kwalara a kasar Sudan ta Kudu kamar yadda ma’aikatar lafiyar kasar ta sanar a yau talata, yayin da ta bayyana cutar mai saurin yaduwa tsakanin al-umma.

wani kenan kwance a asibiti bayan kamuwa da cutar
wani kenan kwance a asibiti bayan kamuwa da cutar REUTERS/Andreea Campeanu
Talla

Ministan lafiya na Kasar, Riek Gaik ya shaidawa taron manema labarai cewa, yanzu haka akwai kimanin mutane 171 da aka tabbatar sun kamu da cutar wadda ta samo asali daga sansanonin ‘yan gudun hijira na Majalisar Dinkin Duniya dake Juba babban birnin Kasar, inda daga nan ta yi ta yaduwa wurare dabam dabam.

Dubban mutane ne dai suka nemi mafaka a sansanonin ‘yan gudun hijiran a lokacin yakin basasan da aka kwashe tsawon watanni 18 ana yi.

A shekarar data gabata, akalla mutane 167 ne a Kasar ta Sudan ta Kudu suka rasu sakamkon cutar kwalarar bayaga dubu 6 da 400 da suka kamu da ita.

To saidai hukumomi sun yi kokarin shawo kan matsalar a wannan lokacin.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.