Isa ga babban shafi
Boko Haram

Najeriya za ta jagoranci rundunar hadin guiwa- Buhari

Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari ya yi watsi da bukatar karba karba na shugabancin rundunar hadin gwiwa da za a kafa ta kasashe biyar da ke makwabtaka da kasar shi domin yaki da Mayakan Boko Haram. Buhari ya ce Najeriya ce ya kamata ta jagoranci shugabancin rundunar.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou da Thomas Boni Yayi na Benin da Idriss Deby na Chadi da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a taron da suka gudanar a Abuja..
Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou da Thomas Boni Yayi na Benin da Idriss Deby na Chadi da Shugaban Najeriya Muhammadu Buhari a taron da suka gudanar a Abuja.. REUTERS/Afolabi Sotunde
Talla

Buhari ya ce tsarin karba karba na iya kawo cikas wajen aikin yaki da Boko Haram.

A ra’ayinsa, Dan Najeriya ne ya kamata ya zama kwamandan rundunar sabanin shawarar da aka kawo na bin tsarin karba-karba duk bayan watanni 6 tsakanin kasashen biyar.

Shugaban Nijar Mahamadou Issoufou da Idriss Deby na Chadi da Bony Yayi na Benin ne suka halarci taron na Abuja tare da wakilin shugaban Kamaru.

Kuma shugabannin sun amince da bukatar Buhari na barin dan Najeriya ya jagoranci rundunar mai dakaru 8,700 har zuwa kammala aikin yaki da Boko Haram.

Shugabannin kuma sun amince Kamaru ta karbi mukamin Mataimakin jagoran rundunar.

Sanarwar da suka fitar bayan kammala taron, shugabannin sun amince rundunar mai suna MNJTF ta fara aiki a ranar 30 ga watan Yuli inda za ta maye gurbin rundunar MNJTF da ta kunshi kasashen Najeriya da Nijar da Chadi da Kamaru da ke yakar Boko Haram tun a watan Fabrairu.

Shugaba Buhari ya sha alwashin murkushe Boko Haram, amma yanzu sama da mutane 150 suka mutu tun bayan rantsar da shi a ranar 29 ga watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.