Isa ga babban shafi
Najeriya

Boko Haram ta kashe mutane 43 a Borno

Mayakan Boko Haram sun kashe mutane akalla 43 tare da kona gidaje da dama a kauyukan Matangale da Buraltima da Dirmanti da ke cikin Jihar Borno a yankin arewa maso gabashin Najeriya. Rahotanni sun ce mayakan sun abkawa kauyukan ne saman Babura tare da wawushe dukiyoyin Jama’a.

Dubban Mutane ke gudun hijira zuwa Nijar daga Najeriya
Dubban Mutane ke gudun hijira zuwa Nijar daga Najeriya AFP/Issouf Sanogo
Talla

Mayakan na Boko Haram sun bude wuta kan mai uwa da wabi a lokacin da suka abkawa kauyukan, kamar yadda wasu mazauna yankin suka tabbatar wa kamfanin dillacin labaran Faransa a yau Alhamis.

Wani mazauni Matangale ya ce ‘Yan Boko Haram sun shigo garin ne da karfe hudu na yamma kafin su shiga Buraltima da Dirmanti.

Rahotanni sun ce daruruwan mutane sun kauracewa gidajensu zuwa Biu wanda ke da nisan kilomita 90 da garin Matangale.

Hare hare kuma na zuwa a yayin da shugaba Buhari ke tattaunawa da shugabannin kasashen da ke makwabtaka da Najeriya kan yadda za a magance matsalar Boko Haram da ke addabar kasashen.

Buhari wanda tsohon Soja ne, ya sha alwashin kawo karshen ayyukan Boko Haram.

Zuwa yanzu kimanin mutane 150 mayakan Boko Haram suka kashe tun lokacin da aka rantsar da Muhammadu Buhari a matsayin sabon shugaban kasa a ranar 29 ga watan Mayu.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.