Isa ga babban shafi
Burundi

Nkurunziza yana nan kan aniyarsa

Shugaban Kasar Burundi Pierre Nkurunziza ya ce babu abin da zai hana shi neman wa’adi na uku duk da zanga zangar da ‘yan adawar kasar ke yi wanda yanzu haka ta yi sanadiyar kashe mutane 5. Mai Magana da yawun fadar shugaban kasar Willy Nyamitwe, ya ce babu abin da zai sa shugaban ya janye aniyarsa saboda kundin tsarin mulkin kasar ya bashi dama.

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza AFP PHOTO/Brendan SMIALOWSKI
Talla

Sakatare Janar na Majalisar Dinkin Duniya Ban Ki Moon ya aike da Jakadansa na musamman Said Djinnit don ganawa da bangarorin siyasar kasar.

Majalisar Dinkin Duniya tace mutanen kasar Burundi sama da 21,000 suka tsere zuwa kasar Rwanda tsakanin Assabar zuwa Lahadi saboda fargabar rikicin siyasa a cikin kasar.

Akalla mutane biyar suka mutu a arangamar da aka yi tsakanin masu zanga-zanga da ‘Yan sanda.

Zanga-zangar dai ta barke ne a Burundi a ranar Lahadi bayan Jam’iyyar CNDD mai mulki ta ba shugaban kasa Pierre Nkurunziza damar neman wa’adi na uku a zaben shugaban kasa da za a gudanar a ranar 26 ga watan Yuni.

Kuma tun a 2005 ne shugaban ke jagorantar kasar, yayin da ‘yan adawa ke bayyana cewa matakin tazarcen ya sabawa kundin tsarin mulki.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.