Isa ga babban shafi
Burundi

Nkurunziza ya ayyana neman wa’adi na uku a Burundi

Ana zaman dar dar a kasar Burundi bayan Jam’iyya mai mulki a kasar ta ba shugaba mai ci Pierre Nkurunziza damar neman wa’adi na uku a zaben shugaban kasa, A karo na biyu a jere, yau matasa a kasar Burundi sun sake fitowa titunan kasar dan adawa da shirin shugaban kasar Pierre Nkurunziza na sauya kundin tsarin mulki dan yin wa'adi na uku. Shugaban dai ya kwashe shekaru 10 a karagar mulki amma sai jam'iyyar sa ta sake tsayar da shi takara a karshen mako..

Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza
Shugaban Burundi Pierre Nkurunziza AFP PHOTO / FRANCOIS GUILLOT
Talla

Rahotanni sun ce tuni dubban mutanen Burundi suka tsallaka zuwa Rwanda da Jamhuriyyar Congo saboda fargabar barkewar rikici a zaben shugaban kasa da za’a a gudanar a ranar 26 ga watan Yuni.

Gungun ‘yan adawar kasar sun sha alwashin cewa za su kaddamar da kazamar zanga-zanga idan har Nkurunziza ya bayyana kudirin sake tsayawa takara.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.