Isa ga babban shafi
Burundi

An yi jerin gwano a kasar Burundi

Dubun dubatar al’ummar kasar Burundi ne suka fantsama akan titunan kasar, don gudanar da Gangamin farin ciki sakin wani fittacce dan jaridar da gwamnatin kasar ta aike gidan yari a cikin kwanakin baya

rfi
Talla

Dubun dubanta yan kasar ne dai sukayi gangami akan tituna babban birnin kasar suna raye-raye da wake-wake, kwana guda bayan sakin Daraktan fittacen gidan Redion kasar na RPA Bob Rugurika daga gidan yari akan beli.

Rahotanni na cewar ba’a bayyana adaddin mutanen da yanda suka fito ba amma wanna adaddi abu ne da ya kafa tarihi a cikin kasar, wanda wasu alumma kasar ke cewa rabon su dasu ga irin wanna taro tun bayan shekrara ta 1993 lokaci da alumma kasar ke bikin samun nasara shugaba Melchoir Ndadaye a matsayin zababben shugaban kasar na farko.

A ranar 21 ga watan jiya ne aka aike da Rugurika gidan yari bayan zargi da akeyi masa da hannu wajen kisan wasu yan asalin italiya 3,

Matakin daya haifar da zanga-zanga tsakanin kungiyoyin farra hula da yan jaridu, wanda ke tahuma gwamnatin kasar da tauye yanci bayyana ra’ayi jarida

An dai yi belin Rugurika ne akan euro dubu 8,400 kwatankwaci kudin kasar miliyan 15, kuma yanzu an cigaba da gudanar da bincike don gano ainihi wadanda suka aikata kisa
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.