Isa ga babban shafi
Najeriya

Zaben Najeriya: Ramalan Yero ya amince da kaye, APC Gombe taki amincewa da sakamako

Har yanzu sakamakon zabukan gwamnoni da aka yi ranar Asabar a Nigeria suna ci gaba da fitowa, inda hukamr zabe ke ci gaba da bayyana sakamkon. Sakamkon zabukan da aka fitar zuwa yanzu sun bayar da mamaki a wasu daga cikin jihohin kasar, kuma tuni wasu daga cikin ‘yan takarar suka fara amincewa da shan kaye, inda suke taya abokatar takarar tasu murna.Rahotanni dake fitowa daga Jihar Kaduna na cewa Tuni gwamna mai barin gado Ramalan Yero na Jami’iyyar PDP, ya taya abokin takarar Shi Nasiru el-Rufai na APC Murnar Nasara a zaben.A nashi bangaren, zababben Gwman el-Rufai ya sake jadda alkwuran da suka yiwa alummar Jihar.Sai dai a Jihar Gombe, duk da cewa hukmar zabe mai zaman kanta ta INEC ta bayyana gwamna mai ci Ibrahim Hassan Dankwambo na jam’iyyar PDP, a matsayin wanda ya lashe zaben, wakilin jami’iyyar adawa ta APC Kabiru Usman, yayi watsi da sakamakon.Amma duk da haka zababben gwamnan ya nemi abokin takarar nashi ya amince da sakamokon.Har zuwa yanzu ana ci gaba da dakon sakamakon zabukan wasu jihohin na Nigeria. 

Zababen gwamnan Jihar Kaduna a Najeriya, Nasir El Rufa'i
Zababen gwamnan Jihar Kaduna a Najeriya, Nasir El Rufa'i Safari News Nageria
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.