Isa ga babban shafi
Amnesty

Amnesty ta bukaci Hukumomin Kamaru su saki dan jarida

Kungiyar Kare hakkin Bil Adama ta Human Rights watch ta bukaci hukumomin kasar Kamaru da su saki wani Dan Jaridar kasar Gerrard Kuissu da suka kama a karshen mako saboda ganawar da ya yi da jami’an ta

Женевьев Гаррио - председатель французского отделения Amnesty International (архив)
Женевьев Гаррио - председатель французского отделения Amnesty International (архив) © Xavier de Torres
Talla

Daraktan kungiyar da ke kula da Yammaci na Tsakiya Afirka Stephen Cockburn ya ce ‘Yan Sanda sun kama Dan Jaridar ne tare da wasu abokan aikin sa uku, amma daga bisani sai suka saki sauran amma shi aka kai shi gidan yari.

Kungiyar ta bukaci baiwa ‘yan jaridu damar gudanar da ayyukan su ba tare da wani shinge ba a cikin kasar.

Matsalar gallaza wa ‘yan jarida a wasu kasashen Duniya dai abu ne mai matukar daukar hankalin hatta Majalisar dunkin Duniya, mai ci gaba da kiraye-kirayen tabbatar da ganin an daidaita al’amurra ta hanyar bari ‘yan jarida su gudanar da ayyukansu ba tare da wani Kaidi ba.

Dai daga cikin manyan matsalolin da ake fuskanta a tsakanin ‘yan jarida musamman a wasu yankunan Nahiyar Afruka ita ce yadda wasu gwamnatoci kan yi amfani da su wajen bata sunan abokan hamayya tare da hanasu baiwa ‘yan adawa damar da ta kamace su.

 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.