Isa ga babban shafi
Najeriya

Amurka ba ta son a samu tsaiku a zaben Najeriya

Gwamnatin Kasar Amurka ta bukaci a gudanar da zaben Najeriya cikin lokaci a yayin da wani bangaren siyasar kasar ke naman a dage babban zaben kasar da za a gudanar a ranar 14 ga watan Fabrairu saboda matsaloli da suka shafi raba katin zabe da kuma barazanar tsaro a yankin arewaci.

Hukumar Zaben Najeriya tace ta shirya tsab domin gudanar da babban zabe a ranar 14 ga watan Fabrairu
Hukumar Zaben Najeriya tace ta shirya tsab domin gudanar da babban zabe a ranar 14 ga watan Fabrairu REUTERS/Akintunde Akinleye
Talla

A cikin wata sanarwa, daga gwamnatin Amurka, kasar tace tana fatar a gudanar da zabe mai tsabta cikin kwanciyar hankali ba tare da wani rikici ba a Najeriya.

A yau Assabar ne hukumar zabe mai zaman kanta a kasar za ta yanke shawarar gudanar da babban zabe ko dage lokacin zaben da za ta gudanar a ranar 14 ga watan Fabrairu.

Kakakin hukumar INEC Kayode Idowu ya ce hukumar za ta jagoranci wani babban taro tare da wakilanta a Jihohin kasar da kuma shugabannin Jam’iyyun siyasa a yau Assabar domin tattauna batutuwan da suka shafi babban zaben.

Sai dai kuma hukumar zaben ta INEC ta karyata wasu rahotannin da ke cewa za ta dage zaben a yau Assabar bayan ta gana da Jam’iyyun siyasar kasar.

Kakakin hukumar Kayode Idowu ya shaidawa kamfanin dillacin labaran Faransa cewa INEC za ta ci gaba da bayar da katin dindin idan har wa’adin da ta diba 8 ga watan Fabrairu ya cika.

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.