Isa ga babban shafi
Libya

Majalisar kasar Libya tayi watsi da sunayen sabbin Ministocin da Fraiminista ya gabatar mata

Majalisar dokokin kasar Libya ta yi watsi da sunayen mutanen da Firaministan kasar Abdullah Al-Thani, mai samun goyon bayan kasashen duniya ya gabatar mata a jiya Alhamis, inda yake neman nada su mukaman Ministoci. A yanzu dai majalisar wadda ke da matsuguni a birnin Tabrouk da ke gabashin kasar tare da firaministan sakamakon barazanar da suke fuskantan daga ‘yan bindiga a birbin Tripoli, ta bukaci Althani da ya sake gabatar da sabbin mutanen da adadinsu ba zai wuce 10 ba a gabanta.Ita dai wannan majalisa da ke takun saka da firaminsitan, an zabe ta ne a cikin watan Yunin da ya gabata, to sai dai sakamakon yadda ‘yan bindiga suka mamaye muhimman cibiyoyin gwamnati a Tripoli, ala dole ta canza mazauni zuwa birnin na Tabruk inda take samun kariya daga wasu mayakan sa-kai da ke yankin.A ranar laraba da ta gabata ne dai Abdallah Althani, ya gabatar da sunayen mutane 18 a gaban majalisar wadanda yake son bai wa mukaman ministoci, to sai dai kakakin majalisar Fradj Abu Hashem, ya ce wakilan majalisar sun ki amincewa da mutanen ba tare da ya bayyana dalilan zabensu ba.Yanzu haka dai kasar ta Libya na ci gaba da fadawa a cikin yanayi na rashin tabbas, a daidai lokacin da kasashen duniya suka zura ido ‘yan tawaye na kara karfi akan yankuna, tsawon shekaru uku da kasar ta share tana fama da yakin basasa. 

Firaministan Libya, Abdullah al-Thani
Firaministan Libya, Abdullah al-Thani REUTERS/Ismail Zitouny
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.