Isa ga babban shafi
Libya

An fara taron neman zaman lafiya a Libya

Gwamnatin kasar Libya ta kaddamar da wani taro da nufin tattauna manyan matsalolin da kasar ke fama da su tun bayar faduwar gwamnatin kanar Mu’ammar Khaddafi. A cewar firaministan kasar ta Libya Ali Zeidan, babbar manufar shirya wannan taro da ke samun halartar wakilai daga sassa daban daban na kasar, ita ce tattauna batun sabon kundin tsarin mulkin kasar, hadin kan al’umma da kuma batutuwan da suka shafi tsaro a kasar.Tun bayan kifar da gwamnatin Moammar Khaddafi, a ranar 20 ga watan Oktoban shekarar 2011, kasar ta libya ke fuskantar tashe tashen hankulan da ke neman jefa ta cikin yake yake. 

Ministan tsaron kasar libya Mohammed al-Bargathi
Ministan tsaron kasar libya Mohammed al-Bargathi Reuters/Esam Al-Fetori
Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.