Isa ga babban shafi
Liberia-Najeriya

Hukumar lafiya ta ce dubbai za su kamu da Cutar Ebola nan gaba a Liberia.

Hukumar Lafiya ta Majalisar Dinkin Duniya wato WHO a takaice, ta ce dubban ‘Yan kasar Liberia ne za su kamu da cutar nan ta Kabari kusa wato Ebola a cikin makwanni masu zuwa

Au Libéria, un habitant du quartier de West Point à Monrovia, mis en quarantaine pour contenir l'épidémie reçoit de la nourriture du Pam, le 28 août 2014.
Au Libéria, un habitant du quartier de West Point à Monrovia, mis en quarantaine pour contenir l'épidémie reçoit de la nourriture du Pam, le 28 août 2014. REUTERS/2Tango
Talla

Hukumar tace wannan kuwa lura da yadda jami’an kula da lafiya 152 suka kamu da cutar kuma 79 daga cikinsu tuni sunriga sun mutu.

‘Yan kasar ta Liberia da dama na fuskantar barazanar kamuwa da cutar ganin yadda wadanda ake zargin sun kamu, ke mu’amala da sauran jama’a ba tare da kariya ba.

Ya zuwa yanzu dai inji Hukumar, mutane sama da 1,000 suka mutu sakamakon kamuwa da cutar a yayin da a dayan bangaren Cutar ke ci gaba da yaduwa zuwa wasu sassan kasar.

Najeriya dai na daga cikin kasashen da ake fargabar kazamcewar al’amarin, inda sakamakon Cutar ta Ibola hukumomi a kasar suka bada sanarwar karin kwanakin hutun Dalibai.

Jihohin Legas da Fatakwal da ke kan iyaka da gabar Teku ne Cutar ta fi kamari a kasra ta Najeriya.
 

LabaranSamun Labaran RFI, Hirarraki, Rubattattuun Labarai, Labarai game da wani, shirye-shirye.

Ku saurari dukannin labaran duniya ta hanyar sauke man hajar RFI

Rarbawa :
Babu shafi

Babu bayanan da ka bukata ko kuma sam babu su.